13 Afirilu 2026 - 22:41
Source: ABNA24
Hizbullahi: Ba Zamu Saurara Ba Ba Zamu Mika Wuya Ba Fagen Yaƙi Zayyi Bayani 

Shugaban Hizbullahi Lebanon: Burin Isra'ila A Bayyane yake shi ne ƙoƙarin ruguza karfin Lebanon da Gwagwarmaya a ƙoƙarinta na shirin samar da babbar Isra'ila. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sheikh Naeem Qasim: Mun yi watsi da duk wata tattaunawa da gwamnatin Sahayoniya masu cin zarafi; wadannan tattaunawar ba su da amfani kuma suna son sauya ra'ayin Lebanon daga rashin son tattaunawa zuwa ga yin tattaunawa kai tsaye. Wannan salon jerin rangwamen gwamnati na kyauta da gwamnatin Lebanon ke bawa Isra'ila, wanda a aikace yana tabbatar da cewa suna da lahani da cutarwa, wanda hakan ya zama wulakanta ga Labanon, gwamnati da al'umma. "Kuna cewa kuna son a tsagaita wuta, amma su me suke cewa kuma wane kayan aikin matsin lamba kuke da shi? Ku zo mu fuskanci keta iyaka tare sannan mu yi tattauna game da komai zai zo a gaba da sauran batutuwa. Abun da muka yanke shawararsa a gwagwarmaya shi ne ba zamu zauna zugum ba ba kuma zamu mika wuya ba; filin daga shi zai yi magana. Sakatare Hizbullah: Mun jimre na tsawon watanni 15 yayin da "Isra'ila" ba ta aiwatar da ko da sashi ɗaya na yarjejeniyar a ranar 27 ga Nuwamba, 2024 ba, duk da haka, mun jira. 

Sheikh Naeem Qasim: Diflomasiya ba ta ci gaba ko da mataki daya ba amma ta'addancin Isra'ila ya ci gaba da saurin gaske tare da cikakken goyon bayan Amurka. Burin 'yan mamaya na Isra'ila a bayyane yake, wato rusa duk wani iko a Lebanon. Waɗannan tattaunawar ba su da wani amfani kuma akwai buƙatar al'ummar Lebanon su taru akan canzata. Tattaunawa wani tsari ne na rangwame kyauta. Idan aka ci gaba da keta iyakr ta'addaci, za mu fuskance shi kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Muddin gwamnati ta taimaka wajen saukaka manufofin ta'addanci, za a ci gaba da ta'addanci ne. Wannan yaƙi ne na Lebanon kan abokan gaba na Isra'ila-Amurka, ba yakin wasu ba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha